Wasu rahotanni na bayyana cewar an samo gangar jikin wani mataccen mutum, a ciki gidan dan wasan tsakiya na kasar Masar, wanda yake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Mohamed Elneny, a gidan sa dake can kasar Masar.
Mahaifin dan wasan mai suna Nasser, shi ya gano gawar mutumin, yayin da ya tsaya a gidan dake garin Mahalla al-Kubra, wanda yake da tazarar kilomita 100, tsakanin sa da Arewacin babban birnin Masar (North of Cairo).
Tuni dai aka sanarda hukumar 'yan sandan garin kan faruwar lamarin, inda bincike yake nuna alamun cewar mutumin da aka tsinci gawarsa a gidan ya jene da niyar satar wayoyin wutan lantarki, sai wutar ta jashi wanda hakan yayi sanadiyar mutuwarsa.
Gidan sabone wanda dangin shi dan wasan Elneny, suka mallaka wa kungiyar da suke taimakawa, gajiyayyu wajen domin su mayar dashi ofishin su.
Dan wasan Mohamed Elneny, wanda a kwannan nan ne ya koma kungiyarsa ta Arsenal, bayan ya wakilci kasarsa ta Masar a gasar cin kofin nahiyar kasashen Afirka, ya samu labarin faruwar wannan lamarinne ta wayar salula.