Dubun Dubatan Farar Hula Ne Rikicin Mali Ya Raba Da Muhallansu

Matasa a Mali suke zanga-zangar kan yadda gwamnatin kasar take daukar hare haren 'yan tawayen abzinawa.

Rahotanni daga kasar Mali na cewa rikicin da ‘yan tawayen Abzinawan Arewacin Mali keyi yayi sanadiyyar korar dubun Dubatar farar hula sun zama‘yan gudun Hijira a kan iyaka da Jumhuriyar Nijer.

Rahotanni daga kasar Mali na cewa rikicin da ‘yan tawayen Abzinawan Arewacin Mali keyi yayi sanadiyyar korar dubun Dubatar farar hula sun zama‘yan gudun Hijira a kan iyaka da Jumhuriyar Nijer.

A tattaunawar da muryar Amurka tayi da iyalan Mali cikon na dubu biyu da suka tsallaka zuwa kauyen Gaoudel dake kan iyaka da Nijer na cewa mayakan ‘yan tawayen Abzinawa ne suka tilasta masu yin kaurar tilas, kuma da yawa na barin kauyukansu dake Arewaci, basu kuma da isasshen abinchi da ruwan sha.

Mafi yawan ‘yan gudun Hijirar Mali suka ce sun yi asarar kadarorinsu a dalilin rikicin Abzinawan Mali. Djibril Oualid yana gtare da iyalinsa yace tafiya suke yi da kafarsu har tsahon kwanaki uku kafin su isa kan iyakar Niger. Ya kara da cewa‘yan tawayen sun kassara kasar Mali, saboda mayakan ‘yan tawayen suna bin farar hula ne suka kwakkawce masu kaya da abinchi da kudi.

Yace shi ya isa zangon kan iyaka ne tare da matarsa da ‘ya’yansa basu da komai duk ‘yan tawayen Abzinawan Mali sun kwace. A watan Janairun da ya gabata ne mayakan ‘yan tawayen Abzinawan Mali suka fara kaiwa farar hula farmaki suna yekuwar sai lallai a basu ‘yancin cin gashin kansu.