Dubban yan kasar Rasha sunyi gangami

Masu zanga zangar nuna rashin amincewa magudin zabe a birnin Moscow kasar Rasha

Masu zanga zangar nuna rashin amincewa magudin zabe a birnin Moscow kasar Rasha

Yau asabar dubban mutane suka yi gangami a Moscow baban birnin kasar Rasha domin nuna rashin amincewarsa ga zargin da suke yi cewa an tupka magudi a zaben wakilan Majalisa da aka yi a kasar a kwanan nan.

‘Yan sandan Moscow sunce akalla mutane dubu ashirin ne suka halarci ganganmin, kodayake shedun ganin da ido sunce mutanen da suka fito sunfi dubu ashirin.

Makoni biyu da suka shige dubban mutane suka halarci gangamin makamancin wannan a Moscow da wasu biranen kasar, yan kwanaki bayan da aka ayyana cewa jam’iyar United Rasha ta Prme Minista Vladimir Putin ce ta lashe zaben.