Yawan 'yan gudun hijira dake kwararawa cikin kasar Slovenia daga iyakarta da kasar Croatia ya tilasta mata daukan matakin tura 'yansanda da sojoji bakin iyakar da nufin takaita bakin hauren da ke shiga kasar.
WASHINGTON DC —
Dubban ‘yan gudun hijira ne suka shiga kasar Slovenia tun ranar Asabar, wanda hakan ya tursasawa kasar daukar matakintakaita kwararar bakin ta kan iyakarsu daga kudancin kasar.
Jami’an Slovenia sunce kimanin ‘yan gudun hijira dubu hudu ciki har da jarirai da kananan yara ne suka shiga kasar a jiya Talata daga Croatia.
Wannan adadi kuma kari ne akan mutane dubu takwas da suka isa kasar a ranar Litinin. Shugaban kasar Borut Pahor yace karin ‘yan sanda za su isa kan iyakar kasarsa da Croatia.
Sannan za su kai karin sojoji duk domin shawo kan lamarin na kwararowar bakin hauren da ya wuce kima.