Dubban Mutane Sun Tserewa Gidajensu a Mozambique

Bairro Carioca Pemba, província de Cabo Delgado, Moçambique

Dakarun tsaro a Mozambique na ci gaba da yaki da rikicin mayaka da ke karuwa a arewacin kasar, inda tashin hankali ya yi sanadiyyar kisan daruruwan farar hula ya kuma tilastawa dubban mutane tserewa daga gidajensu.

Tun daga shekarar 2017, mayakan masu tsananin kishin addinin Islama, da wasunsu ke da alaka da kungiyar ‘yan ta’addan IS, sun kaddamar da hare-hare akan farar hula da dakarun gwamnati a arewacin Lardin Cabo Delgado.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, 11 cikin gundumomi 16 da ke lardin da galibin mazaunansa Musulmai ne sun fuskanci hare-hare da mayakan suka dauki alhakin kaiwa.

Kungiyar wadda aka fi sani da al-Shabab, Ahlu Sunna wa Jama a kasar, ita ce kungiyar ‘yan ta’addan da ta kai hare-hare a Cabo Delgado.

Ana dai daukan kungiyar a matsayin mayakan Mozambique da ke da alaka da IS.