Dubban Mutane Sun Halarci Jana'izar Gama Gari Da Aka Yi A New Zealand

Dubban mutane sun tattaru yau Jumma’a don jana’izar gama gari da aka yi a wata makabarta a New Zealand inda aka binne mutane 26 cikin 50 da suka rasa rayukansu a harin kan mai uwa da wabin da aka yi a wani masallaci ranar Jumma’ar da ta gabata. Mai mafi karancin shekaru a cikin mutanen shine wani yaro dan shekaru 3 da haihuwa.

Da safiyar yau, a wani taron addu’oi da aka yi a wani masallaci dake tsallaken wurin da aka kai mummunan harin na Christchurch, Imam Gamil Fouda ya yi jawabi ga dubban jama’ar da suka taru.

Fouda yace, "muna da nauyin zuciya amma hakan ba zai karya mana gwiwa ba. Muna raye, kuma muna tare. Mun kudiri aniyar ba za mu bari wani ya kawo mana rarrabuwa ba.”

Ya kuma yaba da Firayin ministar New Zealand Jacinda Arden akan abin da ya kira “karfafa iyalansu da ta yi” da kuma yadda ta mutunta su ta hanyar daura dan kwali a lokacin da je jajanta masu. Ya ce shugabancin firayin minister wani abin koyi ne ga duniya.

Mata a fadin New Zealand sun daura Kallabi yau Jumma’a don nuna goyon bayan su ga al’ummar musulman kasar.