Dr. Isa Odidi Da Dr. Amina Odidi Za Su Yi Abin Tarihi

Dr. Isa Odidi tare da Dr. Amina Odidi a lokacin da kamfaninsu na IntelliPharmaceutics ya saye wani makeken kamfanin sarrafa magunguna na kasar Canada a shekarar 2009.

Kwararrun masana kimiyyar magungunan 'yan asalin Najeriya, zasu kada kararrawar bude kasuwar hada-hadar hannayen jarin kamfanonin fasaha ta NASDAQ gobe jumma'a a New York

Kamfanin hada-hadar hannayen jarin kamfanonin fasaha ta NASDAQ a nan Amurka, ta gayyaci Dr. Isa Odidi da mai dakinsa Dr. Amina Odidi, domin su kada kararrawar bude wannan kasuwa gobe jumma'a a New York a nan Amurka.

Dr. Isa da Dr. Amina Odidi, sune shugabannin kamfanin sarrafa magunguna na kasar Canada mai suna IntelliPharmaceutics Inc, daya daga cikin manyan kamfanonin sarrafa magunguna dake kasar. Wannan kamfani, yana cikin kamfanonin da ake sayar da hannayen jarinsu a kasuwar ta NASDAQ, da kuma kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Toronto a kasar Canada.

Dukkansu biyu kwararru ne a fannin harhada magunguna.

Dr. Isa Odidi da Dr. Amina Odidi, zasu zamo 'yan Najeriya na farko da aka taba karramawa da wannan iko na bude kasuwar ta NASDAQ.

Masanan guda biyu sun fito daga Jihar Kano a arewacin Najeriya. Dukkansu biyu sun samu digirinsu na farko a fannin harhada magunguna daga Jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria. Sun kuma samu digiri na biyu da na uku, watau PhD a fannin kimiyyar harhada magunguna daga Jami'ar London.

Kamfaninsu na IntelliPharmaceutics kamfani ne da ya kware wajen sarrafa magungunan hadiya wadanda ke kunshe da wasu sinadarai masu jinkirta shigar maganin cikin jiki har zuwa lokacin da ake bukata. Kamfaninsu ne kadai yake da wata irin fasahar sarrafa magunguna da ake kira "Hypermatrix" a turance, kuma yana da magunguna na cuce-cuce kamar na zuciya, jijiyoyin aikewa da sakonni, ciwon jiki, kashe wkayoyin cuta da sauransu.