Dr. Bukola Saraki Ya Gurfana Gaban Kwamitin Da'a Na Majalisar Dattawa

Dr. Bukola Saraki shugaban Majalisar Dattawan Najeriya da ya gurfana gaban kwamitin da'a na majalisar domin a bincikeshi akan zargin shigo da mota da takardun jabu

Makon jiya ne jami'an kwastan suka cafke motar shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Dr. Bukola Saraki akan zargin cewa an yiwa motar takardun jabu na biyan kudin harajin shigowa da ita cikin kasar

Motar da ake takaddama a kai an sayeta ne akan kudi Naira miliyan dari biyu da tamanin da tara wadda aka ce ta shugaban Majalisar Dattawan Najeriya ce, Dr. Bukola Saraki.

Yau shugaban ya bayyana a gaban kwamitin da'a da sauraren koke-koken jama'a na Majalisar inda ya kare kansa da shigowa da wata motar sulke kirar Range Rover da aka ce an yi mata dakardun bogi.

A cewar Dr. Bukola Sarki 'ni ba mai shigo da motoci ba ne kuma babu lokacin da na shigo da wata mota kirar Range Rover. Kamar yadda kuka sani wannan mota ba ta karan kaina ba ce. Mota ce da aka saya da sunan Majalisa" Ya kara da cewa ko baya kan kujerar shugabancin Majalisar duk wanda yake kanta zai yi anfani da ita.

Kwamitin ya gayyato Mr. Lanre Shittu wanda shi ne ya shigo da motocin daga kasashen waje. Injishi kamfaninsa ya shigo da motocin ne wa Majalisa. Yana mai cewa "babu lokacin da muka taba sayowa Dr. Bukola Saraki mota ta karan kansa"

Majalisar Dattawan ta baiwa kwamitin dake binciken wannan maganar makwanni hudu ya mika rahotonsa.

Yanzu dai an sa ido a ga yadda binciken zai kaya.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Dr. Bukola Saraki Ya Gurfana Gaban Kwamitin Da'a Na Majalisar Dattawa - 1' 37"