Dr. Bugaje Yace Obasanjo ne Ya Jefa Najeriya Cikin Halin Da Kasar Ta Shiga.

Tsohon Shugaba Olunsegun Obasanjo

Dr. Usman Bugaje wanda jigo kuma har ya rike mukamin sakatare jam’iyyar dake mulkin Najeriya a zamanin yakin neman zabe kuma mai sharhi kan harkokin yau da kullum, ya yi tsokaci a kan batun kira da wasu yan Najeriya ke yi na sake fasalin kasar saboda gaggauta ci gaba.

Wannan batu yana ci gaba da jawo muhawara a duk fadin kasar inda ke ganin sake tsarin kasar shine zai kai ta ga samun nasara, wasu kuma na ganin yunkuri ne na mayar da hannun agogo a baya.

A lokacin da ya kawo ziyara a wannan gidan radiyon, Dr. Usman Bugaje yace akwai bukatar a gyara ga fasalin kasar, amma tilas abi tafarkin da kundin tsarin mulkin mulkin kasar ya gindaya tun da farko.

Sai dai ya dora alhakin tabarbarewar al’amura a kasar kan rashin shugabanci, musamman matakai da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya dauka bayan ya kasa samun tazarce.

Your browser doesn’t support HTML5

DR USMAN BUGAJE