Fadar shugaban kasar Amurka-White House ta ce shugaban Amurka Donald Trump zai yi magana da shugabannin Najeriya da Afirka ta Kudu ta wayar tarho a yau Litinin.
WASHINGTON D.C. —
Tattaunawar da shugaba Trump zai yi da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari ya na daukar hankali saboda ba a ji daga Buhari ko kuma ganinsa a bainar jama’a ba tun da ya tafi jinya London ranar 19 ga watan Janairu.
Sabon shugaban kasar Amurka bai yi magana a kan Afrika ko kuma batutuwa da suka shafi Afrika ba tun da ya hau karagar mulki a watan da ya shige.
Babu wani bayani daga fadar White House kan abinda shugabannin za su tattauna a kai.
Bisa ga tsarin aikin Fadar White House, Trump zai tattauna da Buhari da karfe 3:45 agogon Najeriya, kana ya tattauna da shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma da karfe 5:10.