WASHINGTON, DC —
Babban kalubale da iyali ke fuskanta a Najeriya banda koma bayan tattalin arziki da ya shafi kowanne bangaren rayuwa, shi ne matsalar tsaro da kwarru su ka yi harsashen cewa, zai iya haddasa karancin abinci da mai yiwuwa ya kai ga yunwa a wadansu sassan Najeriya, matsalar da yanzu haka take barazana ga harkokin ilimi musamman a arewacin kasar da ake ci gaba da fuskantar garkuwa da daliban makaranta.
Ta haka shirin Domin Iyali ya gayyaci masu ruwa da tsaki domin yin nazarin wannan matsala da kuma neman hanyar shawo kanta, da nufin ba manyan gobe damar samun ilimi da zai taimaki rayuwarsu, ya inganta matsayin iyali da kuma ci gaban kasa.
Saurari tattaunawar da Baraka Bashir ta jagoranta:
Your browser doesn’t support HTML5