DOMIN IYALI: Rahoto Na Musamman Kan Yi wa Rahma Hussein Ahuwa- Satumba, 02, 2021

Alheri Grace Abdu

A ranar Juma’ar Makon jiya ne gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi yafiya da afuwa ga wata matashiya, mai suna Rahma Hussaini dake Unguwar Brigade a Kano, wadda babbar kotun Kano ta yankewa hukunci kisa a shekara ta 2014 bayan samun ta da laifin kashe mijinta ta hanyar soka masa wuka a cikin sa.

Matakin gwamnan ya biyo bayan amincewa da shawarwarin kwamitin shugaban kasa kan yiwa daurarru afuwa, da kuma hukumomin kula da gidajen gyaran hali na Kano. Abinda shirin ya maida hankali a kai ke nan wannan makon.

Saurari cikakken shirin:

Your browser doesn’t support HTML5

DOMIN IYALI:Rahoto Na Musamman Kan Yi wa Rahma Hussein Ahuwa-10:00"