DOMIN IYALI: Matan Najeriya Da Zaben 2023-Kashi Na Daya, Yuni, 30, 2022

Alheri Grace Abdu

Bayan kammala zabukan fidda gwani a shirin babban zaben kasa na shekara 2023 a Najeriya, za a iya cewa, duk da yake mata kalilan sun yi tarihi a bana da suka hada Hussaina Akila Banshika macen farko da ta kai matsayin Darektar labarai a Radiyo Najeriya cikin sama da shekaru 35 da kafa tashar, da Saneta Aisha Binani da ta zama mace ta farko da aka zaba a matsayin ‘yar takarar gwamna a jihar Adamawa, da wata matashiya ‘yar shekaru 28 Jennifer Ndubuisi, da ta kada Eneh Jane Chinwendu mace ‘yar’uwarta a zaben fidda gwanin zuwa majalisar dokokin jiha a mazabar Awgu ta arewa a jihar Enugu, da kuma mata hudu da suka lashe zaben fidda gwani zuwa majalisar wakilai da kuma na jiha a Bayelsa karkashin tutar jam’iyar PDP, Za a iya cewa har yanzu burin mata na samun kaso 35 cikin dari na guraban siyasa a kasar bai cika ba, domin bisa ga alkaluma, kawo yanzu, abinda su ka samu bai kai kashi goma cikin dari ba.

Batun da shirin Domin Iyali ya fara haska fitila ke nan wannan makon.

Nigerian Women and 2023 elections

Bakin da muka gayyata domin nazarin lamarin da neman mafita sun hada da Madam Eneh Ede ‘yar fafatukar kare hakkokin mata, kuma wadda ta tsaya takara a matsayin mataimakiyar gwamna a jihar Binuwe a zaben da jam’iyarta ta sha kaye, da ‘yar gwaggwarmaya Barrister Hassana Ayuba Mairiga,, da kuma dan siyasa a jihar Kano Nasir Shuaibu Marmara.

Saurari kashin farko na tattaunawar da wakiliyarmu a birnin tarayya Abuja Medina Dauda ta jagoranta:

Your browser doesn’t support HTML5

DOMIN IYALI: Matan Najeriya Da Zaben 2023-Kashi Na Daya-10:00"