Wani abinda ya fara zama ruwan dare a tsakanin ma'aurata musamman matasa da 'yan boko shi ne yawan mace macen aure. Yayinda a al'adun kasashen Afrika iyaye sukan shiga tsakani da nufin sasanta ma'aurata idan aka sami sabani dake barazana ga dorewar auren, kasashen da suka ci gaba sukan nemi taimakon kwararru domin samun masalaha.
A Yau shirin Domin iyali ya gayyaci kwararru a fannin zamantakewar al'umma musamman ma'aurata da nufin bada gudummuwa ga wannan yunkurin. Muna kuma tare da Malama Maryam Lemu da kuma Barrister Mainasara Kogo Faskari.A cikin tattaunawar da wakiliyarmu Halima Abdulra'uf ta jagoranta, Maryam Lemu ta fara da bayyana abinda ta ke gani yake janyo yawan mace macen aure.
Saurari cikakken shirin:
Your browser doesn’t support HTML5