DOMIN IYALI: Koma Bayan Ilimin ‘Ya’ya Mata A Ghana-Nuwamba, 03, 2022

Alheri Grace Abdu

Binciken da Bankin Duniya ya gudanar game da ilimin mata a shekarar 2018, na nuni da cewa, kashi 89 cikin 100 na 'yan mata a kasashen duniya suna kammala karatunsu na firamare, sai dai kashi 77 cikin 100 ne kawai suke kammala karatun sakandare. Binciken ya ci gaba da cewa, rashin ba ‘ya’ya mata damar samun ilimi mai zurfi yana janyowa kasashe asarar kudi tsakanin dala tiriliyan 15 zuwa dala tiriliyan 30 kowacce shekara.

Yau shirin Domin Iyali zai fara haska fitila a arewacin kasar Ghana, yankin da ake fuskantar koma bayan ilimin ‘ya’ya mata. Kafin mu kai ga hada kan masu ruwa da tsaki domin neman sanadi da kuma mafitan mun fara da yin shinfida da rahoto na musamman da wakilinmu Idris Abdullah Bako ya hada mana:

Saurari rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

DOMIN IYALI: Koma Bayan Ilimin ‘Ya’ya Mata A Ghana