WASHINGTON, DC —
Matsalar fyade da ta ke ci gaba da zama babban kalubale a Najeriya ta nakara daukar hankalin al’umma a ciki da wajen kasar. Lamarin da ya kai ga kungiyoyin mata da suka hada da matan gwamnoni da kwamishinonin ma’aikatun kula da harkokin mata, jagorantar gangamin neman ganin hukumomi sun dauki kwararan matakan shawo kan wannan matsala da ke nema ta zama bala’i.
A ci gaba da haska fitila kan mummunar dabi’ar, yau shirin domin iyali ya yi hira da barrista Badiha Abdullahi Mu'azu wadda ta jima tana bin diddigin wannan batu a kotu, ta kuma bayyana wa wakiliyarmu Baraka Bashir cewa, duk da ganganin da ake yi, babu alamar sauki
Saurari cikakken shirin
Your browser doesn’t support HTML5