WASHINGTON, DC —
Yayinda ake kara kira ga hukumomi su dauki tsauraran matakan shawo kan matsalar fyade a Najeriya, 'yan fafatuka da masu kula da lamura na ci gaba da tsokaci kan shawarar da gwamnatin jihar Kaduna ta yanke na dandake wadanda aka samu da wannan laifin.
A cikin hirarta da Shirin Domin Iyali, 'yar gwaggwarmaya Hajiya Rabi Salisu Ibrahim wadda take fafatuka wajen ganin bayan wannan lamarin ta ce aiwatar da wannan dokar na iya gamuwa da cikas.
Saurari cikakken shirin