DOMIN IYALI:Bibiya Kan Kafa Dokar Dandaka a Jihar Kaduna-Kashi Na Hudu, Oktoba, 22, 2020

Alheri Grace Abdu

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci hukumomi su sake nazarin dokar da gwamnatin Kaduna ta kafa na dandake wanda aka samu da laifin fyade, dokar da ta sami goyon bayan 'yan fafatuka suka yaba da bayyana goyon baya.
Sai dai gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa, ba zata yi kasa a guiwa ba a wajen aiwatar da wannan doka da kuma kare hakkokin wadanda ake zalunta.

A cikin hirarta da shirin Domin Iyali, kwamishinar ma'aikatar harkokin mata ta jihar Kaduna Hajiya Hafsat Mohammed Baba ta ce an kafa wannan doka ne bisa la'akari da munin laifin da kuma bukatar daukar matakin da zai zama ishara ga masu wannan halin.

Saurari cikakken shirin:

Your browser doesn’t support HTML5

DOMIN IYALI: Bibiya Kan Kafa Dokar Dandaka A Jihar Kaduna-Kashi Na Hudu-10:00"