WASHINGTON, DC —
Makon jiya shirin Domin Iyali ya fara gabatar da batun mutumin nan dan shekaru 50 mai suna Yusuf Bako wanda aka kama yana yi wa wata karamar yarinya 'yar shekaru hudu fyade a masallaci.
Binciken 'yan sanda ya nuna mutumin ya yi zaman kurkuku har sau biyu sabili da samunsa da laifin fyade aka aka sake shi ya ci gaba da yawo a cikin al'umma.
Yau shirin Domin Iyali ya sami yin hira da Sheik Mu'azu Turkunya, limamin masallacin da mutumin ya aikata wannan abin takaici.
Saurari bayanin da limamin Masallacin ya yi mana a hirarshi da wakilinmu Abdulwahab Mohammad.
Your browser doesn’t support HTML5