Tsohon kaftin din Najeriya, Henry Nwosu, yayi kira ga Samson Siasia da ya gayyaci sababbin ‘yan wasan da zasu taimakawa kungiyar sa a wasannin neman zakaran Afirka masu zuwa na shekara ta 2015 Africa Cup of Nations.
Tawagar matasan masu ‘kasa da shekaru 23 dai sun sha kashi a hannun Burkina Faso a wasan kusa da karshe da ake yi na kasashen Afirka a kasar Kongo.
Alokacin da Nwosu ke magana wakilin jaridar Punch, yace kungiyar na bukatar kwararrun ‘yan wasan gaba da zasu rika kai hari, idan har suna son su sami guri a wasannin Olympics da za’ayi na shekara ta 2016.
Ya dai ci gaba da cewa kungiyar na bukatar gyara ga ‘yan wasan baya masu tsaron gida, kasancewar sun sami dama a wasansu na baya amma suka kasa amfani da ita.
Najeriya dai zata kara da kasar Kongo a wasan neman na uku. Zakaran wannan wasa da ke yi a Kongo, zai samu shiga wasannin Rio Olympic da za’ayi na shekara ta 2016, wasannin dai za’ayisu a Sanigal daga 28 ga watan Nuwamba zuwa 12 ga watan Disamba.