Sunday Oliseh yayi kira ga kungiyar Super Eagles ta Najeriya da ta ci gaba da wasan ta a filin wasa na Lagos.
A baya bayan nan Najeriya dai ta karbi bakuncin wasanni a filayen wasa dabam dabam a fadin kasar, wanda hakan ke nuna bambamcin sakamako.
Tsohon dan wasan na Borussia Dortmund Oliseh, yace idan har kungiyar Super Eagles na son zama a gaban kowacce kasa to dole ne suyi wasa a jihar Lagos, domin suna bukatar gurin da za’a matsa musu su horu sosai.
Oliseh dai bayyana cewa bugawa Najeriya wasa yana da sauki a yanzu, ina jin dai hakan ne yasa kungiyar batayin wani abin kirki, ya kara da cewa I dan har za’a yi wasa filin wasan kwallo na Lagos gaban ‘yan kallo dubu dari, har a kai mintuna ashirin ana wasa batare da saka kwallo a raga ba, ‘yan kallo na harzuka sosai, suka tuna iyalan su na zaune a Lagos.
Wannan shine karin matsin lamba, idan kaje wasan cin kofin nahiyar Afirka ko kuma wasan cin kofin duniya kasan cewa duk abinda kayi bai isa ba, to dole kayi wasa babu ji babu gani.
Idan ingila zatayi wani muhimmin wasa suna bugawa ne a filin wasa na Wembley saboda nan ne suke da mafi yawan ‘yan kallo, wanda haka yake saka ‘yan wasa su zama cikin tunani na kada su baiwa magoya baya kunya.