Kungiyar ma'aikatan kananan hukumomin Najeriya ta kafa kwamitin shawo kan majalisun kasar 36 domin amincewa da cin gashin kan kowace karamar hukuma.
Kafin kananan hukumomin su samu 'yanci ana bukatar amincewar a kalla jihohi 24 ko kashi biyu cikin uku na jihohin 36.
Yanzu jihohi ne ke shirya zaben kananan hukumomi da jagorantar harkokin kudi lamarin da shugaban NULGE Kwamred Ibrahim Khalid ya kira aikin babangiwa. Yace zasu cigaba da fafutika cikin lumana a duk jihohin kasar.
Abun da kungiyar zata sa gaba shi ne wayar da kawunan ma'aikatan kananan hukumomin tare da hadawa da addu'oi da ziyarar sarakunan gargajiya da zuwa majalisun jihohi.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5