Najeriya na da tsarin raba arzikin kasa da kan fifita jihohin da ke da arzikin fetur saboda shi ne ke samarwa kasar kudin shiga mafi yawa.
Duk da dai gwamnati ta dade ta na maganar fadada tattalin arziki zuwa sassa waje da man fetur, hakan bai sauya yanda jihohi masu man fetur ke samun kaso mafi tsoka ba.
Wannan samun ba ya nuna talakawa a jihohin na samun wani bambanci tun da farashin kayan masarufi na kara tsada ne.
Masanin tattalin arziki Yusha’u Aliyu ya kawo misalin yanda a ke cewa manoma na kudancewa don hana shigo da abinci amma ta wani bangaren ribar ba ta da cikakkiyar fa’ida.
A ra’ayin gwamna Inuwa Yahaya ga kwamitin bitar rabon arzikin kasa, ya na da muhimmanci gwamnatin tarayya ta sake duba yawan kudin da ta kan rabawa jihohi.
Wani kalubalen a Najeriya shi ne yanda gwamnati ta hana shigo da shinkafa ta kan iyakar kasa amma ta halalta hakan ta bakin teku da jiha irin Lagos ke cin wannan gajiya har ma a ke cewa za ta iya biyan albashi ko ba kaso daga taraiya.
Da babu gara ba dadi, in mai hannu da shuni zai sha miya da nama har da man shanu, talaka ma ya samu miyar ko da wake ne da garin yajin citta sai a zauna lafiya.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5