Shuwagabanin kungiyar kasashen Afirka ta yamma wato ECOWAS na tunanin sanya doka haramta Nikabi, a kasashen su kamar yadda shugaban hukumar ECOWAS, din Kadire Ouedraogo,ya ce.
Ya kara da cewa wasu lokuta ‘yan ta’adda na yin shiga irin ta yadda ba za ‘a gane fuskansu ba hattama jami’an tsaro basu iya tantancen masu irin wannan sutura suje au kuma tafka aika aika wanna dalili ne yasa shugabanin kasashen yammacin Afirkan tunanin daukar wannan mataki cewa a haramta nauo’in siturun da ba’a iya fayyace wadanda suka sasu.
Shugaban hukumar ta ECOWAS Ouedraogo, ya ci gaba da cewa kasashen na ECOWAS,zasu duba wannan batu su kuma duba aladu da irin yanayinsu wajen aiwatar da wanna kudiri dan haramta sanya wadannan tufafi.
A gefe daya kuma tuni Malaman addini sun fara tsokaci kan wannan kudiri na ECOWAS, Ustaz Muhammad Ibrahim Duguri,shine shugaban majalisar Malamai na Kungiyar Izalatul Bidia Waikamatus Sunnah a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.
Yace yana jawo hankalin shuwagabanin ECOWAS akan dokar da ake son sawa domin idan matsala ta taso akan dubi amfani da rashin amfani.
Your browser doesn’t support HTML5