A yau Laraba ne dokar hana kiwo a fili ta fara aiki a jihar Benue. Dokar ta tanadi daurin shekaru biyar a gidan kaso ko tarar Naira miliyan daya ga duk wanda ya saba mata.
Gwamnan jihar, Samuel Ortom, yace manufar dokar ita ce a kawo karshen matsalar tsaro tsakanin makiyaya da manoma a jihar. Dokar ta hana daukan makamai da makiyaya da manoma keyi a jihar.
Mai ba gwamnan jihar shawara kan hulda da manema labarai (NAMES?) ya ce jihar ta sha fama da yawan kisan mutane da lalata miliyoyin dukiyoyi tsakanin manoma da makiyaya. Ya ce rahoton rikicin 2014 ya nuna kananan hukumomi 10 suka yi hasarar dukiyoyi na kimanin Naira biliyan 95 a sanadin wadanan rigingimmun.
Kakakin gwamnatin ya ce dokar ta ba kowa izinin ya mallaki filin da zai dinga kiwo a ciki saboda kiwo sana’a ce. Kamar yadda manomi zai mallaki filin yin gona haka ma ya kamata makiyayi ya mallaki inda zai yi kiwo, wato ya sayi nashi filin. Ya ce ba za’a fifita wani ba bisa wani mutum.
Sai dai sakataren kungiyar Fulani ta Miyetti Allah, Alhaji Baba Usman, ya ce basu amince da dokar ba duk da cewa gwamnan jihar ya zauna dasu sun tattauna akan lamarin.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5