dokar hana fita a jihar adamawa

Police officers stand next to a checkpoint near the site of a Wednesday's blast in Kaduna, Nigeria. Thursday, July 24, 2014.

DOKAR HANA FITA LOKACIN ZABE BA ZAIYI TASIRI BA INJI YAN SIYASA.

Tun farko kwamishinan yan sandar jihar ta Adamawa Mr Gabriel Alhaji wanda shine ya bada sabarwan kafa dokar yace duk wanda aka kama yana karya wannan dokar to zai dandana kudar sa.

‘’Jamaa za a hana fita daga ranar lahadi da yamma sha biyu ga wata, zuwa talata sha hudu ga watan 2015 daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safiya, an hana ababen hawa gaba dayansu zirga-zirga ciki ko harda keke NAPEP masu turin amalanke ko kuma WHEEL BARROW’’

Sai dai yan takaran Gwamna na jamiyyar APC da yan jamiyyar PDMmasu alamar tocila sunce ba zata sabu ba wai bindiga a ruwa.

Dan takaran Gwamna na jamiyyar PDM Dr Ahmed Modibbo ta bakin Darektan kamfe dinsa Barister Sunda Joshua Wilgrade cewa yayi.

‘’Kowa yaci gaba da ayyukan sa tamkar babu doka na hana fitar dare a Adamawa domin bai isa yazo ya kawo muna dokar da babu ba mu kuma muna zargin shi yake son ya haddasa fitina, saboda haka muci gaba da zaman mu na lafiya mu fita mu kada kuria, mu tabbatar kuma mun raka kuriun mu an kirga an bayyana sakamako, ance za ayi zabe daga karfe daya da rabi har sai an kare zabe idan zaben ya kai karfe 6 to yaya za ayi zaice ne a waste sai gobe a dawo aci gaba kirgawa kome?’’

Shima Darektan kamfe na jamiyyar APC Alhaji Abba Jimeta yayi bayanin cewa,’’Su sani anyi zaben shugaban kasa lafiya an bada sakamako jamiyyar APC taci Adamawa kaf babu wani abu da ya faru, sabo da haka idan sunce za a hana fita kafin a fadi sakamakon zaben gwamna, to ya nuna muna kenan suna da wani abu a boye’’

To sai dai ita jamiyyar PDP dake mulki a jihar ta bakin sakataren jamiyyar Barister A T Shehu wanda kuma shine kwamishinar harkokin sharia yace bada yawun su ne aka kafa wannan dokar ba.

‘’Kafa dokar ta baci wannan bai dace ba, maimakon kafa wannan dokar ta baci koda yake sunce hujjar su sunce wai sabo da bayan zabe kada mutane su fita suna murna, maimakon kafa wannan dokar ta baci su jawo wa mutane fitina me zai hana su kafa dokar hana duk wani biki bayan zabe ina ganinshi yafi dacewa’’

Sai dai da aka tambaye shi wannan dokar bada yawun su ba kenan sai ya amsa da cewa’’Ba da yawun mu ba bada sanin mu ba’’

Yayin da haka ke faruwa a jihar Adamawa a makwabciyar ta ko shugabanni ne ke kira ga jamaa da su fito kwan su da kwarkwata su jefa kuriaar su cikin lumana, Honarabul Marafa Bashir Abba sabon dan majilisar dattawa da aka zaba yayi kira ne yana mai cewa.’’Babu kamar zaman lafiya, ina kira ga jamaa na dan ALLAH dan Annabi ayi zamanlafiya zabe kowa yana da abinda yake so ya zaba a ransa yaje ya zaba ya koma gidan sa ya zauna lafiya har abada sakamako ALLAH ke bada mulki’’