An Kafa Dokar Hana Fita A Birnin Maiduguri

  • Ibrahim Garba

Wasu sojojin yaki da 'yan bindiga kenan a jihar Borno

Sojoji sun kafa dokar hana fita ta sa’o’i 24 a sassan birnin Maiduguri na arewa maso gabashin Nijeriya
Sojoji sun kafa dokar hana fita ta sa’oi 24 a sassan birnin Maiduguri na arewa maso gabashin Nijeriya, a daidai lokacin da jami’an tsaro ke cigaba da farautar wadanda su ke kyautata zaton masu tsattsauran ra’ayin Islama ne a yankin.

Yau Asabar sojojin sun bayyana unguwanni 10 na birnin na Maiduguri da ke karkashin dokar hana fitar. Sojojin dai sun killace garin sannan suka katse hanyoyi.

Birnin Maiduguri, inda nan ne kungiyar nan mai tsattsauran ra’ayin Islama Boko Haram ta samo asali, shi ne hedikwatar jihar Borno.

Wani mai magana da yawun Ma’aikatar Tsaron kasar mai suna Chris Olukolade ya fadi yau Asabar cewa sojojin za su cigaba da fafatawa da ‘yan Boko Haram har sai sun zakulo dukkannin ‘yan kungiyar a duk inda su ke.

Jami’ai a Nijeriya sun ce an kashi wasu da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne a garin sannnan an kama wasu 65 tun bayan da sojoji su ka fara kai manyan hare-hare kan ‘yan bindigar a rewacin kasar ‘yan kwanaki da su ka gabata.

Your browser doesn’t support HTML5

Ra'ayi Kan Yadda Ake Aiwatar Da Dokar Ta Baci A Arewa Maso Gabashin Nijeriya - 2.22