Dogaro Da Kai Shine Mutuntaka

An bukaci matasa mata da su nemi sana’ar hannu domin dauke wa ‘iyaye sun wasu dawainiyar gida ko na karatunsu, wata matashiya Aisha Aliyu, ce ta bayyana haka ne a yayin zantawa da wakiliyar dandalinVOA , Baraka Bashir, a shirin zauren mata.

Matashiya Aisha, ta ce da sana’ar kwaliya na make up ga amare da ‘yan mata da masu jego ta ke taimakawa kaninta da mahaifiyarta domin samun damar cigaban karatunsu.

Ta kara da cewa ya zama wajibi ga matasa maza da mata dasu tashi tsaye su nemi sana’ar dogaro da kai domin samun ingantatciyar yaruwa

Ta ce daga lokacin da ta rasa mahaifiyarta ne ya sa ta tashi tsaye kan kafafunta domin share wa kanta hawaye, ta hanyar dauke dawainiyar kaninta da kuma samun damar cigaban karatunta na gaba da sakandare.

Your browser doesn’t support HTML5

Dogaro Da Kai Shine Mutuntaka - 2'10"