A taron manema labarai da direbobin suka kira a wani gari Ogere dake tsakanin Legas da Ibadan sun bayyana cewa sun dauki matakin shiga yajin aiki tun daga ranar Juma'a mai zuwa.
Direbobin suna korafi kan shugabannin kungiyoyinsu da kuma gwamnati akan yadda suka yi kunnen uwar shegu dangane da koken da suka kai masu.
Direbobin sun ce jami'an gwamnatin Legas dake sa ido kan zirga-zirgar motoci ko LASMA sun kashe daya daga cikin direbobin wanda ya ajiye motarsa tsakiyar birnin Legas domin ya yi salla. Direbobin sun bayyana cewa su ne suke shan wahalar dakon mai daga tashar jirgin ruwa dake Legas zuwa sassa daban daban na kasar.
Suna zargin cewa daga gwamnatin jihohi zuwa tarayya babu wanda yake daukansu da mahimmanci saboda haka ne jami'an tsaro ke musguna masu a koina ba tare da an dauki wani mataki ba..
Kwamred Umar Fulani na daya daga cikin direbobin takokin yace jami'an LASMA sun ja dan'uwansu daga layi sun takashi da mota. Sun jira su ga an yi wani abu ba'a yi ba. Suna jayayya ne akan hakkokinsu da aka tauye.
Shi ma Kwamred Umaru Adamu cewa ya yi suna kiran gwamnatin tarayya ta ja kunnuwan gwamnatocin Legas, da Ogun da Oyo akan matsalolin da suke samu.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5