Direbobi Sun Zargi 'Yansanda da Yi Masu Kwace da Cin Zalin Fasinjoji A Taraba

Ibrahim K. Idris babban sifeton 'yansandan Najeriya

Shugaban kungiyar direbobin Najeriya Malam Abubakar Mairiga yace direbobin da suke bin hanyar Adamawa da Taraba su ne suke fuskantar matsalar kwace dac in zalin fasinjoji

Malam Mairiga ya gayawa Muryar Amurka cewa direbobinsu suna kawo masu korafin cewa idan sun zo shiga Jalingo jihar Taraba suna samun matsaloli masu yawan gaske da 'yansanda.

Inji shi 'yansanda na tare direbobin su sauke fasinjojin dake cikin motocinsu kana su soma tambayar wani katin zabe ko shaidar zama dan kasa kuma ko mutum nada su 'yansandan zasu fito masu ta wata hanya daban da zasu cutar da mutane.

Idan a cikin mota akwai Fulanin da suka kai goma sai direba ya bada kudi kimanin nera dubu ishirin kafin 'yansandan su bari ya wuce. Sau tari su Fulanin ne suke tara kudin direban ya biya.

Wani direba mai suna Abubakar Sani yace shi ganao ne dangane da irin tursasawar da 'yansandan ke yiwa fasinjoji musamman Fulani. Ya lissafa wuraren da 'yansanda ke yi masu hakan.

Malam Sani yace da zara 'yansandan sun ga Fulani a mota ko wani da yayi kama da bakauye sai su ce sai ya biya nera dari biyar ko nera dubu su kuma dinga yin barazana da ankwa da bindiga suna cewa su ba 'yan Najeriya ba ne. Yace shi kansa an taba karbar nera dubu ukku a hannunsa.

Wani bafillace yace sun kusa shiga garin Jalingo makonni biyu da suka wuce sai 'yansanda suka taresu suka ce su kawo takardun shaidar zama dan kasa kana suka ce sai kowannensu ya basu nera dubu goma goma. Daga karshe sai da suka biya nera dubu ukku ukku kafin a barsu su shiga Jalingo.

Saidai ta bakin DSP Mshelia kakakin hukumar 'yansandan jihar Taraba yace zargi ne kawai ake yiwa 'yansandan amma zai bincika.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Direbobi Sun Zargi 'Yansanda da Yi Masu Kwace da Cin Zarafin Fasinjoji A Taraba - 3' 34"