Direbobi Sun Koka Da Karbar Na Goron Jami’an Tsaro a Adamawa

Wata mota dauke da jama’a

Cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a tsakanin jami’an tsaron Najeriya kamar yadda wasu Fasinjoji suka bayyana. Direbobin haya sun kawo misalin yadda ake takura musu a hanyoyinsu na zuwa garuruwa daban-daban.

An sha samun rahotannin yadda ake samun kace nace tsakanin jami’an tsaron da fararen hula matafiya a motocin haya wadanda yawanci masu karamin karfi ne, amma duk da haka jami’an sun zurawa aljihunsu idanu don karbar na goro.

Wani lokacin irin wadannan cece ku ce din har ta kan zama fada ta yi sanadiyyar ka ji ance jami’an sun lakadawa direba ko yaron mota kashi sakamakon kin bada na Oga da yaransa. Kai an ma sha samun rahotannin wasu jami’an sun yi harbi don an hana na goro.

Abinda ya fi damun matuka motocin hayar shine, yadda gwamnati ta ce kar su karbi cin hanci amma sai sun karba. Wasu wuraren ma sun ce z aka ga an rubuta a kwalelen allon kan hanya kusa da jami’an cewa kar a bada cin hanci laifi ne.

Amma idan ka bi dokar ka kuma yi kokarin buga wayar da aka ce ka kai kararsu, to za kuwa ka sha na Jaki kafin ka sami kai rahotonsu. Ga rahoton wakilinmu Ibrahim Abdulaziz daga jihar Adamawa.

Your browser doesn’t support HTML5

Direbobi Sun Koka Da Karbar Na Goron Jami’an Tsaro a Adamawa - 2'08"