De Rossi Zai Bar Roma

De Rossi

Dadadden dan wasan tsakiya, wanda ya shafe gaba daya rayuwarsa tun da ya fara buga kwallon kafa har zuwa yanzu a kulab din garinsu wato kungiyar kwallon kafa ta Roma da ke Italy, zai sauya kungiya a kakar wasannin da za’a fara a badi.

Daniel De Rossi, ya shafe shekaru 18 ya na bugawa kungiyar ta Roma tamaula da zai cika a karshen wannan kakar wasannin ta bana.

Amma ya kasa bin abin da shahararran dan wasannan Francesco Totti ya yi da ya yi ritaya a mutumin da ya bugawa kungiya daya tilo.

Sai dai kulab din da yake buga gasar Serie A ya tabbatar cewa, dan wasan tsakiyar mai shekaru 35 da haihuwa zai bar kungiyar yayin da kwantiraginsa zai kare a karshen wannan kakar wasannin.