Staffan de Mistura ya fadawa manema labarai a New York ta wayar tarho da daren jiya Talata daga Otal, cewa wadanda suka shirya zaman tattaunawar da suka hada da Rasha da Iran da kuma Turkiya kowanensu sun bashi shawarar sunayen mutanen hamsin, wakilan kwamitin da za’a kafa. Yace za su hada da wakilai daga gwamnatin Syria da na yan adawa da ma masu zaman kansu.
De Mistura yace ya himmantu wurin tabbatar da kwamitin kundin tsain mulkin. Sai dai kwararen jami’in na diplomaisya bai bada bayani akan lokacin da kayyade na sanar da tsarin da yayi ko ranar da kwamitin zai fara zaman shirya kundin tsarin mulkin.
Ya kuma tabbatar da cewa aiki dake gabanmu yana da sarkakiya. Amma kuma yace su imanin za’a iya samun ci gaba daga nan.