Dawo Da PDP Karagar Mulkin Najeriya Kuskure Ne - Ribadu

Tsohon shugaban hukumar EFCC, Malam Nuhu Ribadu (Hoto: Shafin Nuhu Ribadu na Twitter)

Tsohon shugaban hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya, Malam Nuhu Ribadu, ya nuna fargabar cewa dawowar jam’iyyar adawa ta PDP karagar mulki zai iya maido da hannun agogo baya ga abin da ya ce gagarumar nasarar da aka samu a fannin yaki da cin hanci.

Ribadu wanda shi ne babban jami’in tuntunba na kamfen din ta-zarcen shugaba Muhammadu Buhari, ya ce aikin yaki da cin hanci da gwamnatin APC ta yi, ya fi duk abin da PDP ta gudanar a tsawon shekaru 16 da ta yi tana mulki.

"Ka ga mutum shi kadai, duk duniya yana da gida a ko ina, kana da shi a Ingila kana da shi a America, kana da shi a Dubai. Mutumin da ya yi shekara uku ya zo ya kawo canji a rayuwarmu, za ka ce in cire shi, in dawo da wanda ya yi min lalaci, duk irin nadamar da ya yi, ai ni ba wawa ba ne." inji Ribadu.

Kalaman nasa na zuwa ne kwanakin kadan kafin 'yan Najeriya su yi zaben shugaban kasa.

Sai dai babbar jam'iyyar adawa ta PDP, ta ce, kushe ta da APC ke yi, alamu ne na rashin adalci da kuma rashin hujjar rashin cika alkawuran kamfen da hakan ya jefa ‘yan Najeriya cikin kunci.

"A kasar nan, babu tsaro, babu abinci, babu ayyuka, tattalin arzikin kasa ya lalace, matasa sai shaye-shaye, kai har harkokinmu da kasashen waje ya tabu. To idan aka ce wannan gwamnati ta komo ta sake shekara hudu, sai mu ce Najeriya Allah ya sawwake in akwai ta." Inji Sakataren PDP na kasa, Sanata Umar Tsauri.

Tuni dai hukumar zabe ta fara tura kayayyakin zabe da hakan ke nuna ba damuwar dage zaben kamar yadda aka gani a 2015.

Saurari cikakken rahoton Sale Shehu Ashaka daga Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

Dawo Da PDP Karagar Mulkin Najeriya Kuskure Ne - Ribadu - 2'24"