Davutoglu Ya Dora Laifin Hari Akan ISIS

davutoglu ny

Firai Ministan Turkiyya, Ahmed Davutoglu, ya fadi yau Litinin cewa kungiyar ISIS ce aka fi zarga a binciken da jami'ai ke yi, na gano wadanda su ka kai tagwayen hare-haren nan na ranar Asabar a birnin Ankara, wadanda su ka yi sanadin mutuwar mutane 97

Davutoglu ya ce hukumomi na dab da gano daya daga cikin maharan, kuma alamomi na dada nuna yatsa kan, abin da ya kira "wata takamammiyar kungiya."

Fashe-fashen da su ka tarwatsa wani gangamun kiran a yi zaman lafiya, sun kuma raunata mutane 160, a harin, wanda ba a taba yin mai muninsa ba a tarihin Turkiyya.

Davutoglu ya ce manufar harin shi ne a kawo cikas ga zaben da za a gudanar ranar 1 ga watan Nuwamba a Turkiyya, to amma za a gudanar da zaben kamar yadda aka tsara.

Gabanin nan, Firayim Ministan ya yi kira ga mutanen kasar da su hada kai wajen yakar ta'addanci, amma ba tare da daukar nauyin harin ba, kungiyoyin da ke gaba da juna a Turkiyya, sun yi ta dora laifin kan juna.

'Yan Majalisar Dokoki daga jam'iyyar AKP mai mulki, sun yi zargin cewa fashe-fashen wata kullalliya ce ta 'yan awaren Kurdawa da ke son a tsani gwamnati, a yayin da wasunsu kuma ke zargin jam'iyyar HDP ta Kurdawa da kai hari kan magoya bayanta a wurin gangamin, don ta kara samun goyon baya a zaben.