Jama’a, bayan kafar Ungulu da kungiyar ManU tayi wa David Moyes, to yau Laraba dai ya fito yayi magana. Shine ma yake cewa:
"Kasancewa Manajan Manchester United, daya daga cikin manya-manyan kulob a duk fadin duniya abu ne wanda zan jima ina alfahari da shi.
Karbar ragamar kungiyar bayan nasarori iri-iri na tsawon lokaci mai tsawo da tayi, dama na san babban kalubale ne, kuma nayi alfaharin karbarta kuma bani tantama ko daya na yin hakan.
Wato wahalar aikin zaman Manaja a United babba ne sosai, amma ban taba ja da baya ba, daga aiki tukuru, ni da abokan aikina. Na gode musu da irin zuciyar da suka nuna, da imani da sukayi akaina tsawon season din da ya wuce.
Mun mayar da hankulan mu matuka wajen gani mun sake gina kungiyar, kuma mun yi hakan ne a dai-dai lokacin da muke samar da sakamako masu kyau a gasar Firimiya da Champions. Sai dai a wannan lokaci na sauyi, sakamakon da aka samu ba shine ManU da magoya bayanta suka saba da shi, kuma suke tsammani kuma gaskiya na fahimci ko mene ne ya ci musu tuwo a kwarya."