Inji Kanar Almajir shekaru arba'in da biyu da suka gabata aka mayar da bikin tunawa da samun 'yancin kai na dasa itace saboda yanayin kasar.
Kanar Almajir wanda ya kasance babban darakta na ma'aikatar gandun daji ta jihar Damagaran ya bayyana cewa a shekarar 1960 kasar ta samu kubuta daga mulkin mallakar Faransa. Yace Nijar kasa ce ta Sahel dake da karancin itace idan kuma ba'a maida hankali ga dasa itace ba hamada zata mamaye kasar.
Taken bikin bana shi ne a dasa itace cikin gonakai saboda samun albarkar gona. Ice cikin gona na kara albarkar gona.
A tsawon shekarun da aka yi ana dashen itatuwa babbar matsalar da aka samu ta jibanci itacen dalili ke nan da mahukuntan kasar suka gargadi jama'a da zara sun dasa itace su dinga gadinsa har ya shekara. Haka ma ake watsa jiyawa ta tsiru domin ta taimakawa kasa.
Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5