A wani matakin nuna bacin ran su da halin da jahar su ta Adamawa ta fada ciki saboda dambarwar siyasar neman tsige gwamna da mataimakin shi, dimbin kungiyoyin mata, da na matasa da kuma na 'yan kasuwar jahar ne suka yi wata zanga-zangar lumana har zuwa fadar gwamnan jahar a garin Yola:
Your browser doesn’t support HTML5
Zanga-zangar lumanar ta gudana ne a lokacin da kwamitin mutum bakwai da babbar kotun jahar ta kafa ya ce ya kammala bincike a kan gwamna Murtala Nyako da mataimakin shi Bala james Ngilari.
Kungiyoyin sun ce sun shirya zanga-zangar lumanar ce domin su bi sahun Sarakuna da shugabannin addinan jahar wadanda suka yi kira ga 'yan majalisar dokoki da ma duk wani mai hannu a cikin dambarwar siyasar, da su tausayawa al'ummar jahar, su sasanta saboda halin kunci da ha'ula'in da ake ciki a jahar.
Yanzu haka dai al'amuran rayuwar yau da kullum da hada-hadar kasuwanci da cinikayya sun tsaya cak a jahar ta Adamawa saboda rashin kudin biyan albashin ma'aikata sakamakon rufe asusun jahar ta Adamawa da hukumar EFCC ta yi, kuma babu wanda ya san ranar da hukumar za ta saki asusun.
Wakilin Sashen Hausa na Amuryar Amurka a jahar Adamawa Ibrahim Abdulaziz ne ya aiko da rahoton.