Daruruwan makiyaya,mahauta ,manoma dama sauran fataken dabbobi ke nan yayin wannan zanga-zangar lumanan da suka yi har zuwa majalisar dokokin jihar Taraban domin nuna rashin amincewar su da sabon kudurin doka da gwamnatin jihar ke neman kafawa da zai hana kiwo fili.
Kungiyoyin da suka karade Jalingo fadar jihar, sun bukaci yan majalisar dokokin jihar da su yi fatali da wannan kudurin doka da gwamnan jihar Darius Dickson Isiyaku ya tura musu.
Alh.Bashir Sambo Garkuwan Lamire shugaban hadakar kungiyar yan kasuwa –Manoma ta arewa ya bayyana dalilansu na shiga wannan zanga-zangar.
Da suke mika takardar koken nasu shugaban kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah na jihohin arewa maso gabas Umar Mafindi Danburam da kuma takwaran aikinsa na jihar Taraban Sahabi Mahmud Tukur sun koka da cewa ba’a tuntube su ba, kafin gwamnan ya mika wannan batu ga majalisar dokokin jihar.
Kakakin majalisar dokokin jihar, Abel Peter Diah shi ya tarbe su koda yake daga bisani an tashi dutsi a hannun riga , yayin da kakakin majalisar ya nemi kare manufar wannan kudurin doka.
Batun da suke zargin cewa da lauje cikin nadi ,koda yake kakakin majalisar yace ba haka zance yake ba.
Ita dai wannan dokar zata hana kiwo a fili,kuma duk wani makiyayin da zai shigo jihar sai ya samu izini yayin da za’a tanadar da rundunan ko ta kwana dake zama dogarawan hana kiwon,wanda yanzu kuma lokaci ne kawai ke iya tabbatar da yadda zata kaya!Kungiyoyin da suka karade Jalingo fadar jihar ,sun bukaci yan majalisar dokokin jihar ne da su yi fatali da wannan kudurin doka da gwamnan jihar Darius Dickson Isiyaku ya tura musu.
Alh.Bashir Sambo Garkuwan Lamire dake zama shugaban hadakar kungiyar yan kasuwa –Manoma ta arewa ya bayyana dalilansu na shiga wannan zanga-zangar
Your browser doesn’t support HTML5