Daruruwan 'Yan Najeriya Sun Tsere Zuwa Jamhuriyar Nijar

Wasu 'yan gudun hijira da rikici ya raba da muhallansu a jihar Taraba a wani lokaci a baya

Jihar Zamfara da ke makwabtaka da Nijar ta sha fama da hare-haren 'yan bindiga wadanda a lokuta da dama sukan yi garkuwa da mutane domin neman makudan kudaden fansa.

Kimanin mutum 1,000 ne suka yi gudun hijira daga garin Cigama da ke cikin jihar Zamfara zuwa garin Gidan Ahamad da ke Gundumar Madawa a jihar Tahoua da ke Jamhuriyar Nijar.

Rahotanni sun ce sun tsere ne sanadiyar hare-haren 'yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Wasu daga cikin mutanen da suka tsere, ya fadawa Muryar Amurka cewa ya rasa 'yan uwansa sanadiyar wannan rikici.

Hukumomin karkara, sun kai agajin farko ga 'yan gudun hijira kamar yadda bayanai daga hukumomi suka nuna.

Jihar Zamfara da ke makwabtaka da Nijar ta sha fama da hare-haren 'yan bindiga wadanda a lokuta da dama sukan yi garkuwa da mutane domin neman makudan kudaden fansa.

Saurari cikakken rahoton Haruna Mamane Bako domin karin bayani:

Your browser doesn’t support HTML5

Daruruwan 'Yan Najeriya Sun Tsere Zuwa Jamhuriyar Nijar - 2'02"