Daruruwan Matasa daga Kasashe da Dama Suka Taru a Yamai Babban Birnin Nijar

Matasan da suka taru a Yamai

Matasa da suka fito daga kasashen Afirka ta Tsakiya da kudancin nahiyar ta Afirka da na yankin Maghreb suka hallara a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar domin tattauna matsalolin da suka shafi tsaro da zaman lafiya da batun bakin haure

Matasa maza da mata da suka fito daga kasashen Afirka ta Tsakiya, Kudancin Afirka, yankin Sahel da Maghreb ne suka taru a birnin Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar domin lalubo bakin zaren matsalolin harkokin tsaro, zamantakewa da bakin haure da suka addabi Afirka.

Taron nasu nada nasaba da alwashin da Majalisar Dinkin Duniya ta sha a shekarar 2015 na kare matasan kasashen daga barazanar afkawa cikin wata ta'asa.

Muhammad Haruna na majalisar matasan yana mai cewa kudurin Majalisar Dinkin Duniya ya bada haske bisa ga abun da yakamata a yi domin a shawo kan matsalolin da suka shafi matasa. Dalili ke nan da aka yanke shawarar sa matasa cikin kowace magana da kowane shirin da ya shafi matasan domin a yi nazari dasu su kuma bada gudummawarsu.

Kudurin Majalisar Dinkin Duniya kan matasa ya sa su matasan suka shirya taron da zummar yin nazari akan abubuwan da suka shafeu da yadda yakamata a tunkaresu a tasu fahimtar. Musamman abun da suke dubawa shi ne yawancin bakin haure dake barin nahiyar zuwa kasashen turai a matsayin bakin haure matasa ne. Shin menene yake sasu barin kasashensu su tafi kasashen da basu da wani galihu ko tallafi?

Inji Muhammad Haruna rashin aiwatar da kudurin Majalisar Dinkin Duniya da kasashe suka kasa yi ya harzuka yawan bakin haure ya kuma sa suka kira taron. A taron zasu gano inda aka aiwatar da kudurin da kuma inda ba'a aiwatar dashi ba kuma su san dalili.

Kakakin gwamnatin Nijar Asmanu Malam Isa ya bayyana taron a matsayin wata hanyar tattara shawarwarin matasa a kokarin neman hanyar fita da rikita-rikitan da kasashen Afirka ke ciki.

Shugabannin Matasan kasashe daban daban da na gwamnatin Nijar

Mahalartan taron zasu rubuta wani kundun tsari da zai kunshi shawarwarinsu kana su mikawa shugaban kasar Nijar domin ya gabatar dashi a zauren Majalisar Dinkin Duniya, inji shugaban matasan Nijar Aliyu Umaru

Ga rahoton Souley Mummuni Barma da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Matasa daga Kasashe da Dama Suka Taru a Yamai Babban Birnin Nijar - 2' 26"