Cikin matsalolin da daliban suke korafi a kai har da rashin samun alawus alawus a daidai lokacin da suka ce kudin karatu ya tashi sama a makarantu masu zaman kansu.
Suleiman Muhammad yace shekara daya ke nan da suke ta kai-komo akan a biyasu hakkkinsu amma gwamnati tayi kunne shegu, dalili ke nan da su ma suka fito su nuna rashin jin dadinsu. Baicin hakan idan sun kare karatu ba'a basu aiki sai dai su dinga talla.
Karin kudin makaranta ya hana 'ya'yan talakawa damar samun ilimi idan ba da taimakon gwamnati ba. Rashin biyan alawus ya hanasu iya biyan kudin makaranta. Wai da alawus da ake basu suke biyan kudin makaranta tare da sayen abinci da sayen kayan aiki.
Kungiyar hadakan masu koyon sana'ar hannu ita ta shirya zanga zangar domin tayar da hukumomi daga barci dangane da matsalolin da daliban suka kira dadaddu.
A cewar wani jigon kungiyar Muhammad Sidi Ibrahim zasu cigaba da gwagwarmaya har sai sun ga abun da ya turewa buzu nadi.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5