Ana zargin yan kingiyar ta Hakika,da aikata ayyukan da basu dace da addinin Musulunci ba, kamar masha’a, tu’ammali da kwaya da kuma halasta zina,baya ga barin sallah da zaumi.
Cikin kwanakin nan ne ma hukumomin tsaro a Najeriyan suka bankado bullar wannan sabuwar kungiya ta yan Hakika, da ake zargin wai cikin yan darikar Tijjaniya ta fito, batun da shugabanin darikar a Nigeria ke nesanta kansu da yayan kungiyar ta hakika.
Tun farko hukumomin tsaro sun alakanta bullar kungiyar ne da jihohin Adamawa da Nasarawa,inda ake zargin yan hakika da shan giya,harka da mata da kuma daina salla,da sunan cewa haka darikar ta koyar.
To sai dai kuma yayin da ake ci gaba da bincike game da yayan kungiyar,hadakar kungiyoyin mabiya dariku a Nigeria, na ci gaba da nesanta kansu da ‘yan hakika.
Sheikh Ibrahim Abubakar Daware, dake zama shugaban kwamitin zawiyoyi a Nigeria,ya ce wasu ne ke neman batawa darika suna, don haka ba za su kyale ba.
Shima da yake karin haske, Modibbo Mauludu Bose Tola, ya bukaci hukumomi, musamman jami’an tsaro na ayi taka-tsantsan don kada garin neman gira a rasa ido.
‘Yan kungiyar dai a kwanaki sun soma samun mabiya a jihar Adamawa, musamman matasa da kuma ‘yan mata kodayake wasu sun soma tuba suna ficewa daga kungiyar
Ya zuwa yanzu hukumomin tsaro cewa suke suna kara bincike dongano bakin zaren lamarin. SP Othman Abubakar shi ne kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa daya daga cikin jihohin da ake cewa akwai yan Hakika.
A saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz
Your browser doesn’t support HTML5