Daraktar Hukumar Kiwon Lafiya Ta Duniya Na Ziyara A Najeriya

Margaret Chan, babbar daraktar Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ko WHO, wadda zata kammala wa'adinta a watan Yuin 2017

Dr. Masigiso Muyeti wadda itace daraktan bangaren kiwon lafita a Hukumar Kiwon Lafiya ta duniya ko WHO a takaice wadda zata gaji babbar daraktar hukumar a watan Yunin 2017, ta kai ziyara Najeriya

Yanzu ta fara ganawa da wasu kusoshin ma'aikatar kiwon lafiya ta Najeriya dake Abuja tare da wasu jami'an gwamnati domin gabatar da tsare-tsaren da hukumar zata yi anfani dasu wurin magance wasu manya da kananan cututuka dake yiwa bil Adama barazana.

A wurin ganawar ita Dr Mueti ta jinjinawa yadda Najeriya ta tsara kasafin kudinta akan sha'anin kiwon lafiya tare da fitowa da matakan da zata yaki sauran cututuka. Ta yaba da nasarorin da aka samu akan yakar cutar polio da dai sauransu.

Dr Sani Gwarzo daya daga cikin likitocin ma'aikatar kiwon lafiya ta Najeriya ya yi karin bayani akan ziyarar. Yace ziyarar tana da mahimmanci a mataki daban daban ga kasar. Kodayake sai watan Yunin shekara mai zuwa zata zama shugabar hukumar gaba daya amma ta san irin kokarin da Najeriya ke yi akan kiwon lafiya a nahiyar Afirka.

Zuwanta Najeriya ya ba mahukuntar kasar damar shigar da bukatunsu da zasu zama alheri ga kasar.

Ga cikakken rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5

Daraktar Hukumar Kiwon Lafiya Ta Duniya Na Ziyara A Najeriya - 3' 18"