Darajar Manchester United Da Sauran Kungiyoyi A Nahiyar Turai

Manchester United

An sake bayyana sunan kungiyar kwallon Kafa ta Manchester United ta kasar Ingila a matsayin kulob mafi girma daga cikin kulob kulob din kwallon kafa da suke nahiyar Turai.

Kamfanin kasuwanci ta KPMG, ya yi kididdiga da cewar darajar kungiyar ta Manchester United, ta kai adadin kudi yuro biliyon € 3.25bn kimanin fam biliyon (£ 2.9bn).

Jagoran kamfanin na KPMG Andrea Sartori, wanda kuma marubucin rahotone, kan wasanni, ya ce yawancin kamfanonin kwallon kafa masu duba darajar kungiyoyi sun karu fiye da shekarar da ta gabata.

Kamfanin ya bayyana sunayen kungiyoyi Goma sha shida daga cikinsu duk daga Firimiya lig na kasar Ingila suka fito.

Acikin jerin sunayen kungiyoyi Goma da aka bayyana, Manchester united ta kasance ta farko da darajarta ta kai €3.255bn.

Sai kungiyar Real Madrid, ta kasar Spain wacce darajarta ta kai fam miliyon €2.92bn, sai kuma Barcelona - €2.78bn, Bayern Munich - €2.55bn, Manchester City - €2.16bn, Arsenal - €2.10bn, Chelsea - €1.76bn.

Liverpool wacce ta ke jiran wasan karshe na cin kofin zakarun turai a bana ita ce a matsayi na takwas - €1.58bn, Juventus - €1.30bn daga nan kuma sai Tottenham - €1.29bn.

Your browser doesn’t support HTML5

Darajar Manchester United Da Sauran Kungiyoyi A Nahiyar Turai