Bayan an sanarda tsagaita wuta da hafsan hafsoshin Najeriya yayi shaila akai har ma ya bada oda sojoji su daina yaki sai kuma kwatsam aka ji wasu da sunan kungiyar Boko Haram sun kashe mutane a jihohin Borno da Adamawa da Yobe.
Banda kashe mutane kungiyar ta cigaba da cafke kauyuka tana kafa tutocinta da ikirarin kafa tasu daular. Umar Faruk Musa ya sake neman Danladi Ahmadu inda ya tunkareshi da abubuwan dake faruwa bayan sanarda shirin tsagaita wuta da yace sun cimma.
Danladi Ahmadu ya hakikance cewa an tsagaita wuta. A nashi bayanin wadanda suke kai harin ba 'yan kungiyarsa ba ne. Yace barayi ne. Akwai wasu jami'an hukumomin Najeriya da suke bata sunan Boko Haram. Ba sa son a samu sulhu domin kudin da suke samu daga rikicin.
Dangane da cigaba da kama wasu kauyuka a jihohin Borno, Adamawa da Yobe Danladi Ahmadu yace su basu samu bayani ba. Basu san da 'yan kungiyar dake irin wannan aikaiakar ba. Ya umarci gwamnati ta san yadda zata kama irin wadannan mutanen dake cigaba da fitina.
Danladi Ahmadu yace yana cigaba da yin taro da wasu 'yan kungiyar yana yi masu bayani akan yarjejeniyar da suka cimma. Inji shi, yanzu kungiyar na jiran bayani daga shugaban Chadi akan abun da aka cimma wurin taron da jami'an Najeriya wanda ake zaton an yi jiya Litinin.
Akan 'yan matan Chibok dake hannun 'yan Boko Haram har yanzu Danladi Ahmadu yace gwamnatin Najeriya ce taza gindiya nata sharudan da yadda za'a cikasu kana shugaban Chadi ya sanar da kungiyar kafin a sako 'yan matan.
Sakin 'yan Kamaru da 'yan China da kungiyar tayi yana cikin abubuwan da aka cimma a wurin taron farko da ya hada da Najeriya da kasar Kamaru a Chadi. Dalili kenan da shugaban Chadi ya nemi kungiyar ta yadda ta saki 'yan matan Chibok.
Daga karshe Danladi Ahmadu ya kira wadanda suke cigaba da tayar da kayar baya cewa su daina. Idan basu daina ba za'a daga masu Kur'ani, wato za'a tsine masu ke nan. Yace batun tsagaita wuta da gaske suke yi domin suna son kawo zaman lafiya a kasar Najeriya.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.
Your browser doesn’t support HTML5