Yarjejeniyar da Alhaji Aliko Dangote ya rabtawa hannu ta kunshi kudi na dalar Amurka miliyan dari daya
Kamfanin hada motocin zai hada kimanin motoci dubu goma kowace shekara abun da masana tattalin arziki ke ganin zai habaka tattalin arzikin kasar tare da samar ma dubban mutane aiki.
Dr. Dauda Muhammad Kontagora masanin tattalin arziki da kasuwanci a jami'ar Bayero yace kafa kamfanin nada mahimmanci ga tattalin arzikin kasa saboda baicin samar wa mutane ayyukan yi za'a samu saukin lalacewar manyan motocin idan har sabbi ne..
Ta fannin biyan haraji gwamnatin tarayya zata samu kudaden shiga. 'Yan Najeriya da zasu yi aiki a ma'aikatar zasu samu damar koyon fasahar kere-kere musamman kirar mota. Za'a samu musayar fasaha tsakanin 'yan kasa da 'yan China da zasu zo suyi aiki.
A nashi bangaren Alhaji Muhammadu Baba mai kamfanin motoci mai zaman kansa yace matakin abun yabawa ne matuka musamman game da nufin gwamnatin Najeriya na ganin an fara hada motci a cikin kasar.
Yarjejeniyar ta tanadi cewa kamfanin Dangote zai mallaki kashi sittin cikin dari na kamfanin.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5