A rana ta biyu a shirin jana’izar tsohon Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Anan, an bai wa danginsa damar yi ma gawarsa bankwana ta karshe.
A rana ta biyun, wato jiya, ka’idojin gargajiya ne su ka mamaye hidimar shirin jana’izar tsohon Sakatare-Janar din na Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya mutu da shekaru 80 a duniya bayan wata ‘yar gajeruwar jinya.
Baya ga dangin marigayi Kofi Annan din, Ministoci, ‘yan majalisar dattawa da ‘yan majalisar wakilai, da shugabannin al’umma da sauran masu fadi a ji, wadanda sun ranar da aka kawo gawarsa Ghana su ka fara yi ma ta bankwana ta bangirma, sun cigaba da zuwa su na nuna alhili da kuma yin bankwana ga gawar Annan, a hidimar da ta hada da bushe-bushe da kuma kade-kade na musamman.
Yau Alhamis za a yi wa Annan jana’iza a Ghana, kasarsa ta haihuwa.
Your browser doesn’t support HTML5