Dangantaka Tsakanin Amurka Da China

Shugaban Amurka Donald ya ce ya na zuba ido ya ga an kirkiro wata alaka mai tsari tsakanin Amurka da China.

Wata sanarwa da fadar White House ta fitar jiya Laraba na cewar Trump ya bayyana hakan ne a wata wasika da ya aikewa shugaban China Xi Jinping.

Sanarwar ta kuma ce, Trump ya godewa Xi game da barka da ya masa a lokacin da aka rantsar da shi a cikin watan da ya gabata.

Trump ya kuma yiwa mutanen China barka da bukin shekara na Lantern Festival.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen China Lu Kang ya fada a yau Alhamis cewar China ta yaba da wannan wasikar Trump kuma ta dauri aniyar yin aiki da Amurka don bunkasa yin aiki tare da samar da hulda mafi girma.

Ya zuwa yanzu shugabannin biyu ba su yi Magana da juna ba tun da Trump ya amshi ragama a matsayin shugaban Amurka, sai dai Kang ya ce kasashen biyu na samun zantawa ta kud da kud.

Wani malami a sashen nazarin China a Jami’ar China ta Honk Kong Willy Lam, ya ce ya na ganin China za ta amince da wannan wasikar Trump a matsayin girmamawa duk da dai wasikar ta zo a makare.