Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanarda cewar dan wasanta Malcom zai tafi jinya, na tsawon kwanaki 10, zuwa 15, bayan da dan wasan ya samu rauni a karawar da kungiyar ta lallasa kulob din Cultural Leonesa da ci 4 da 1 a gasar cin kofin sarki (Copa del Rey) a ranar Laraba da ta gabata.
.
Sakamakon tafiyar dan kwallon Barcelona din Malcon, jinya hakan ya nuna cewar ba zai samu damar fafatawa awasan da Barcelona za ta yi da kungiyar Tottenham na kasar Ingila ba, a gasar cin kofin zakarun Turai.
Inda Tottenham za ta ziyarci Barcelona a ranar Talata mai zuwa da burin samun nasara a filin wasa na Camp Nou, wanda hakan shine zai bata damar hayewa zagaye na gaba a gasar daga matakin rukuni.
Haka kuma Malcom ba zai fafatawa Barcelona ba a wasan da zata buga da takwararta Espanyol ba a gasar La-Liga mako na 15 a ranar Asabar.